Gwamnatin Yemen Ta Amince Ta Tattauna da 'Yan Tawayen Houthi

Harin jiragen sama akan Aden kasar Yemen

Harin jiragen sama akan Aden kasar Yemen

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun ce gwanatin kasar Yemen ta amince zata zauna da 'yan tawayen Houthi a karshen watan nan a Geneva, domin su tattauna kan hanyoyin aiwatar da kudurin Majalisar Dinkin Duniya wanda zai kawo karshen yaki da aka yi watanni ana gwabzawa.

Wakilin da Majalisar Dinkin Duniya ta nada na musamman kan rikicin da ake yi a kasar Isma'il Ould Cheikh Ahmed ya rubuta a shafin Facebook cewa an cimma matsaya kan gudanar da taron ne bayan da aka yi shawarwari da shugaban kasar wanda yake gudun hijira a Saudi Arabia, Abdu-Rabbu Mansour Hadi. Daga bisani wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephanie Dujarric ya tabbatar da hakan.

Amincewar ta biyo bayan da kungiyar 'yan tawayen wacce Iran take daurewa gindi ta amince a hukumance makon jiya cewa zata aiwatar da kudurin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya bukaci kungiyar ta janye daga biranen kasar data kama a fada da suke ta gwabzawa tun bara.

Ahalinda ake ciki kuma,sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, ya fada jiya Litinin cewa, zai gana cikin makon nan da shugabanni daga kasashen Rasha, da Turkiyya da Saudiyya, da kuma Jordan domin su tattauna kan duba yiyuwar sake farfado da shawarwari kan hanyoyin cimma maslaha ta fuskar siyasa a rikicin da ake yi a Syria.

Mr.Kerry ya fada lokacinda yke ziyara a kasar Spain cewa, Amurka bata son ganin rugujewar Syria baki daya.