Gwamnatin Togo Ta yi Murabus

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton take ganawa da shugaban Togo Faure Gnassingbe, a fadar shugaban kasar.

Ba zato ba tsammani Friministan kasar Togo da Gwamnatin da yake yiwa jagorancin sun bada sanarwar yin murabus,bayan sun yi ‘yan watanni suna aiki.

Ba zato ba tsammani Friministan kasar Togo da Gwamnatin da yake yiwa jagorancin sun bada sanarwar yin murabus,bayan sun yi ‘yan watanni suna aiki.Ba kuma wani dalilin da friminista Gilbert Fossoun da majalisar Ministocin Gwamnatinsa suka bayar da yasa suka yi murabus tun daga daren larabar da ta gabata.

Sai dai wani dan jarida mai zaman kansa, Ebow Godwin, dake Lome, babban birnin kasar Togo ya shaidawa Muryar Amurka cewa dalilin murbus din ba zai rasa nasaba da zaben kananan hukumomi da na alkalai da za a yi cikin watan Oktoban bana ba.

Sabuwar dokar zabe a Togo na cewa duk wani dake rike da matsayi a Gwamnatin Togo, yake kuma son takarar zaben majalisar dokoki mai zuwa, lallai ne ya fara yin murabus daga matsayinsa a Gwamnatin kafin cika takardun neman yin takara.

Don haka tana yiwuwa ke nan friministan yayi murabus ne domin yin aiki da abinda dokar zaben ta tanadar tunda yana son yin takara zabe mai zuwa.