Ministan yace matakin ya shafi makarantun gwamnati da wadanda ke zaman kansu. Tsawaita hutun zai bada damar horas da malamai da samar da naurorin auna jini domin duba yaran cikin matakan yakin.
Ministan yace idan aka bari cutar ebola ta bulla a kowace makaranta domin inda aka tara yara dubbai zai zama da hadari. Idan sun koma gidajensu Allah kadai ya san irin barnar da za'a haifar. Kafin yara su koma makaranta ranar 13 ga watan Oktoba kowace makaranta firamare ko sakandare za'a dauki malamai guda biyu ma'aikatan asibiti su basu bita. Tun daga bakin kofar makaranta za'a dauki matakan bincike. Akwai wata naura idan mutum ya zo kusa za'a iya auna zafin jikinsa. Idan zafin jikin mutum yayi nisan da ya wuce misali za'a killaceshi tun daga bakin kofa a je a yi cikakken bincike a asibiti.
Dangane da yadda matakin zai yi tasiri a makarantun islamiya, wato tsangaya, da kuma abun da malaman makarantun keyi domin dakile yaduwar cutar ta ebola, Shaikh Abdulahi Bala Lau yayi bayani. Yace suna tattaunawa da kwararrun likitoci wadanda suka san ciwon da illarsa. Kwanan nan kungiyoyin likitoci musulmai suka tuntubeshi akan cutar. Amma duk wani matakin da gwamnati ta dauka zasu bada hadin kai domin ba umurni ba ne da ya sabawa Allah ko manzonsa. Umurni ne da zai taimakawa lafiyarsu da kiwon lafiyarsu. Zasu yi duk abun da zai taimakawa makarantunsu domin a kare yara da al'umma daga fadawa cikin muguwar cutar.
Shaikh Bala Lau ya kara da cewa yadda gwamnati ta dauki matakan hana yaduwar cutar ebola yakamata ta dauki matakan kawo karshen kashe-kashen dubban mutane da a keyi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5