Gwamnatin Najeriya ta tashi haikan wajen karfafa gwiwar 'yan gudun hijirar Boko Haram da ke komawa gidajensu da su ka gudu su ka bari.
WASHINGTON, D.C. —
A yinkurinta na sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar Boko Haram da ke dawowa garuruwansu, gwamnatin tarayyar Najeriya ta shiga samar masu da tallafi gadan-gadan a wuraren da su ke a fadin kasar.
Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, wanda hadimin Shugaban kasa Ibrahim Baba Fatel ya jagorance ci ya ce abin da gwamnati ta sa gaba a yanzu shi ne sake tayar da komadar masu dawowar.
Wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar da ke dawowar sun ce abubuwa sun fara kyautatuwa, to amma har yanzu sun a fama da karancin kayan bukata. Don haka sun yi kira ga gwamnatoci da sauran wadanda abin ya shafa da su tashi haikan wajen agaza masu.
Your browser doesn’t support HTML5