Gwamnatin Taayyar Najeriya Ta Bukaci Sarakunan Gargajiya Su Rungumi Jama'arsu

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ziyara

Yayinda ya je nadin sarautar sarkin Shagamu a jihar Ogun mataimakin shugaban Najeriya ya bukaci sarakunan gargajiyan Najeriya da su rungumi jama'arsu domin samun zaman lafiya da ci gaban kasa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci sarakunan gargajiya su rungumi jama'arsu tare da tabbatar da dawamammen zaman lafiya a yankunasu.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo shi ya yi kiran a garin Shagamu dake jihar Ogun a wajen nadin Akarigbon kasar Remo Sarki Adewole Ajayi.

Farfesa Osinbajo ya ce dole ne mulkin sabon sarkin ya hada duk kawunan 'yan yankin Remo domin a ciyar da kasar gaba,kasa mai dimbin tarihi. Inji mataimakin shugaban Najeriya, hadin kawunan jama'a yana kawo zaman lafiya da ci gaban kasa da inganta tattalin arziki.

Shi ko gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun ya umurci sabon sarkin ya yiwa jama'arsa jagoranci mai kyau, ya yi duk abun da zai yi ya tabbatar da zaman lafiya a yankinsa kana ya ilmantar da jama'arsa akan mahimmancin biyan haraji.

Gwamnn ya ba sabon sarkin tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta mara masa baya domin samar ma jama'a duk abun da ake bukata.

Da yake mayar da jawabi sabon sarkin, Akarigbo Adewole Ajayi ya ce zai yi duk abun da zai yi domin kare babban matsayin da aka dora masa. Ya yi alkawarin gudanar da mulkinsa da adalci da tsare gaskiya da mutunci.

Sarakunan gargajiya da dama ne suka halarci nadin

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Taayyar Najeriya Ta Bukaci Sarakunan Gargajiya Su Rungumi Jama'arsu - 2' 44"