Gwamnatin tarayyar zata tuntubi gwamnatocin arewa maso gabas domin lalubo hanyar da za'a bi a rarraba dalibai zuwa wasu makarantu kafin sha'nin tsaro ya inganta a yankin.
Ministan ilimin Najeriya Ibrahim Shekarau ya shaidawa wakilin Muryar Amurka shirin gwamnatin tarayyar a wurin yaye daliban Jami'ar Jihar Gombe da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.
Yace sha'anin tsaro ya addabi kowa a kasar. Sabili da haka zasu ziyarci gwamnatocin jihohin da abun ya shafa su san hikimar da su keyi akan tanadin da suke yiwa dalibansu. Idan ba zasu iya karatu a inda suke ba gwamnatin tarayya zata daukesu ta kaisu wasu makarantu ko na gwamnatin tarayya ko na wasu jihohi su cigaba da karatunsu har harkokin tsaro su inganta.
Yayin da yake yin nashi jawabin gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya taya daliban murnar samun kammala karatunsu. Ya gargesu su yi anfani da ilimin da suka samu wajen yiwa al'umma aiki. Yayi yi masu hannunka mai sanda akan irin kalubalen da zasu fuskanta nan gaba.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.
Your browser doesn’t support HTML5