Mukaddashin shugaban Najeriya Parfessa Yemi Osinbajo ya tabbatarwa shugabannin kabilar Igbo cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya zata dauki dukkan mataki da ya wajaba wajen ganin ta kare ‘yanci zama da walwalar ko wani dan Najeriya yayi zamansa babu tsangwama a ko wani bangare na kasar.
Mr. Osinbajo, ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da shugabannin kabilar Igbo, bayan da yayi irin wannan ganawar da shugabannin arewa.
Wannan matakin ya biyo bayan wa’adi da matasan arewa suka baiwa ‘yan kabilar Igbo su bar arewacin kasar, saboda fafutukar da suke yi na neman a kafa kasar Biyafara.
Da yake magana da manema labarai bayan taron, Gwamnan jahar Ebonyi David Umahi, wanda yana daya daga cikin shugabannin kabilar Igbo da ya halarci taron, yace sako da zai baiwa masu fafutukar neman a kafa kasar Biafra shine, ‘yanci ne ga ko wani dan kasa yayi fafutuka, muddin za’a yi shi cikin lumana . Gwamna Umahi yace ko mutum da iyalinsa ana fafutuka tsakaninsu kan kudin chefene.
Wannan matsalar ta ‘janyo martini daga sassar Najeriya daban daban.
Wata kungiyar makiyaya da ‘yan kasuwa dake kudu maso gabashin kasar tayi Allah wadai da wa’adin da kungiyar matsana arewan suka baiwa ‘yan kabilar Igbo.
Haka itama, wata kungiyar ‘yan kasuwa dake arewacin kasar tayi Allah wadai da wa’adin da ‘yan arewan suka baiwa ‘yan kabilar ta Igbo.
Your browser doesn’t support HTML5