Gwamnatin Tarayya Ta Yiwa Masana'antu Tanadin Sarafa Kayansu da Yadda Zasu Samu Kasuwa

Irin kayan da kananan masana'antu ke sarafawa a jihar Filato

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo ya fada a Jos jihar Filato irin tanadin da gwamnatin tarayya ta yiwa manya da kananan masana'antu yadda zasu sarafa kayansu su kuma samu kasuwar sayar dasu

Farfasa Yemi Osinbajo ya kaddamar da shirin tallafi wa matsakaita da kananan masana'antu da gwamnatin tarayya ta fito dashi.

Shirin an fito dashi ne ta yadda kanana da matsakaicin masana'antu zasu iya samun lamunin kudade cikin sauki da rangwame da samun horo da shawarwari akan yadda zasu inganta sana'o'insu.

A cewar mataimakin shugaban kasar Farsa Osinbajo gwamnati ta hada kawunan hukumomi dake da ruwa da tsaki a harkokin masana'antu da suka hada da hukumar tantance abinci da magunguna da hukumar tabbatar da sahihancin kaya da bankin masana'antu da gidauniyar horas da masana'antu da sauransu domin saukin sarrafa kaya.

Mataimakin shugaban yace yanzu haka hukumar kwastan ce kadai zata dinga duba duk wata hajja da za'a shigo da ita kasar sabanin da da hkumomi da dama ke daukan lokaci suna gudanar da binciken.

Farfasa Osinbajo yace zasu tabbatar cewa duk wanda zai yi kasuwanci a kasar zai iya yi ba tare da wata matsala ba.

Gwamnan jihar yace gwamnatin jihar ta shirya domin hadin kai da bankin masana'antu domin samar wa kananan masana'antu Naira biliyan biyu na inganta sana'o'onsu. Haka kuma zasu cigaba da horas da matasa sana'o'i domin inganta tattalin arzikin jihar da kasa ma gaba daya.

An bazaz kolin abubuwan da mutane suka kirkiro har da tiraktoci da sassan mutum.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Tarayya Ta Yiwa Masana'antu Tanadin Sarafa Kayansu da Yadda Zasu Samu Kasuwa - 3' 32"