Sakataren labarun PDP Oliseh Metuh yace dama APC bata da wani kwakwaran tsari na tattalin arziki haka kuma tana anfani da kotuna a kokarin kwace wa PDP wasu jihohi kamar Rivers da Akwa Ibom da Taraba da dai sauransu da nufin mayarda kasar mai jam'iyya daya.
Garba Shehu mai ba shugaban kasa shawara kan labaru ya yi watsi da zargin. Yace banbancin mulkin Shugaba Buhari da gwamnatin da ta shude ke nan. Idan abu baki ne zai ce baki ne. Buhari ba zai yi rufa-rufa ba akan Najeriya a kasashen waje. Yace abun da PDP ke so shi ne idan shugaban ya fita waje ya dinga yaudara amma shi ba zai yi hakan ba. Idan tattalin arzikin Najeriya bashi da lafiya zai fada. Babu kudin kashewa amma a dinga bada kwangiloli ana watanda da dan abun da ake dashi ba tafiyar Buhari ba ke nan.
Hukunce-hukuncen kotunan sun yiwa wasu 'yan PDP dadi a wasu sassa yayinda wasu kuma suka yi korafi. Haka ma lamarin yake da 'yan APC.
Shahararren matashin PDP Ado Buni Yadi yace hukunci kotuna da suka ba PDP nasara a wasu jihohin ba abun mamaki ba ne. Ya yi misali da jihar Yobe.
A bangaren APC wani matashi na ganin daukaka kara shi ne mafi a'ala ga duk wadanda basu gamsu da hukuncin kotu ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5