An Kama 'Yan Kasar China Dana Najeriya Kan Hakar Ma'adinai A Jahar Flato.

Minista Kayode Fyemi daga tsakiya.

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin a kama shugaban kamfanin Solid Units Alhaji Abdullahi "Dan China."

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanini da suke hakar ma’adinai a jahar Flato ba tare da izini ba, kuma ta ayyana shugaban daya daga cikin kamfanoni da suke aiki a wuri da ake kira zirak, a zaman wanda take nema ruwa a jallo.

An kama ‘yan kasar China 8 ciki harda wasu ‘yan Najeriya.

Ministan ma’adinai Kayode Fayemi, wanda mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Babagana Mungono ya rufawa baya, yace ya ayyana aiki da dokar hakar ma’adinai ta Najeriya ta shekara ta 2007, wajen dakatar da aikace-aikcen kamfanonin hakar ma’adinai da kamfanonin Solid Units da kuma Jotex a jahar Flato.

Minista Kayode yace, gwamnatin tarayya tana neman Alhaji Abdullahi Adamu Usman, mai inkiya dan China ruwa a jallo. Shine shugaban kamfanin Solid Units, wadanda suke aiki ba tareda izini ba.

Da yake magana, Gwamnan jahar Flato Simon Lalong, ya bayyana farin cikinsa kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.

Mazauna yankin sun bayyana jin dadin daukar wannan mataki da fatar gwamnatin tarayya zata samar musu da kayan more rayuwa. Kamfanonin suna ta kwasar arzikin Najeriya ba tareda samarwa mazuana yankin kayan more rayuwa da kuma ayyukan yi ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Kama masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.