Gwamnatin Tarayya ta daga matsayin babban asibitin tarayya na kasa dake Keffi

Maikatan asibiti suna lura da mara lafiya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba asibitin tarayyar dake Keffi jihar Nasarawa izinin fara jinyar masu ciwon sikila kafin karshen shekara.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba asibitin tarayyar dake Keffi jihar Nasarawa izinin fara jinyar masu ciwon sikila kafin karshen wannan shekarar.

Sanarwar da ta fito daga hannun jami’in hulda da jama’a na asibitin malam Jamil Nagogo ta bayyana cewa, ministan lafiya farfesa Onyebuchi Chukwu ne ya sanar da bada izinin a ranar yaki da cutar sikila ta bana, inda ya bayyana cewa, an yi nisa da shirin domin cimma nasara. Ya kuma bayyana cewa, za a rika yiwa masu cutar sikila jinya kyauta.

Tun farko ma’aikatar ta bada irin wannan izinin ga asibitai biyar da suka hada da na jihohin Gombe, da Ebonyi da kuma Lagos a yunkurin inganta aikin jinya a kasar.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa, majalisar likitocin magani da na hakori ta Najeriya ta daga matsayin asibitin zuwa cibiyar zurfafa kwarewar ikin magani domin likitocin jinya musamman wadanda suke aiki a jihar Nassarawa.

Za a bukaci likitoci su rika zuwa samun horo a asibitin domin samun maki ishirin da suke bukata na horo kowacce shekara na sabunta lasisinsu na aiki.

Da wannan daga matsayin asibitin da aka yi, za a iya gudanar da tarukan karawa ma’aikatan jinya sani, da sauran taruka da kuma ayyukan da suka shafi jinya.