Manufar raba wadannan baburan ko masu taya 3 masu dibar kaya shine farfado da komadar tattalin arzikin al’ummomin da suka koma yankunan su da aka kwato daga hannun yan bindiga masu tada kayar baya na boko haram.
An fara rarraba wadannan ne da kananan hukumomi 7 da sune suka fara fadawa hannun ‘yan bindigan.
Da yake jawabi wajen raba wadannan banburan Gwamnanjihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindowa Umar ya bayyana makasudin kaddamar da wannan shirin inda yay aba wa shugaba Muhammadu Buhari wajen samar da wadannan kekune yace yunkuri ne na musammam domin tallafawa wadanda suka huskancin iftilain boko haram.
‘’Wannan lokacin na farko in so nayi was hi shugaba Muhammadu Buhari godiya domin duk abinda kuka gani anan da taimakon sa ne aka samu kuma ina son in kara wa shi sakataren gwamnatin tarayya Shima ya taimaka kwarai da gaske domin ganin an bada wadannan kekune kafin muma a gwamnatance muka kawo namu gudunmowar wanda shi yasa yau kuke ganin ake wannan shirin’’
Gwamnanyaja hankalin wadanda suka anfana da wannan shirin da suyi wa ALLAH godiya da yasa su suka samu wannan.
Yace idan sunyi wa ALLAH godiya sai kuma ya kara musu.
Ga IbrahimAbdul Azeez da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5