Albarkacin ranar yawon bude ido ta duniya da aka yi ranar 27 ga watan Satunba, masu ruwa da tsaki sun yi jawabi a wajen wani biki da aka yi a tsaunin Mambila dake jihar Taraba a arewa masu gabashin Najeriya.
Taken bikin na bana shine "Yawon bude da ayyuka: makoma mai kyau ga kowa." A wajen bikin an kuma tattauna akan batun samar da zaman lafiya a tsakanin wasu al’ummomin jihar da su ka fuskanci tashin hankali a tsakaninsu a cikin kwanakin nan.
Khadija Umar Dahiru Dorofi, 'yar asalin yankin Mambilla, ta ce bikin na bana ya burgeta, haka su ma wasu da suka je bikin sun bayyana yadda ya burge su.
A wannan yankin ne ake da gandun dajin Gashaka, wato Gashaka Gumti Park. A shekarun baya, akan zo daga kasashen waje domin yawon bude ido ko shakatawa a wurin amma a yanzu lamurra na neman komawa baya.
Lawal Hamidu,na cikin ma’aikatan wannan gandun dajin na Gashaka, ya yi bayani akan irin albarkatun da wurin da kuma abin da ya kamata ayi don farfado da gandun dajin.
Gwamnatin jihar Taraba ta ce a shirye ta ke ta hada hannu da hukumomi, da kungiyoyi na ciki da wajen Najeriya da ma kamfanoni wajen bunkasa harkar yawon bude ido.
Yanzu dai abin jira a gani shine matakan tsaron da za’a dauka don kare masu yawon bude ido, musamman a wannan lokaci da matslar tsaro ke kara ta’azzara a wasu sassan Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5