Gwamnatin Nijar Zata Ragewa ‘Yan Kasar Kudin Wutar Lantarki

Taron masana ilmi a Nijar

[‘Yan Jumhuriyar Nijar masu anfani da wutar lantarki kasa da kilowatts hamsin zasu samu rangwame, a cewar majalisar ministocin kasar a taronta na karshen shekara

Biyan kudin wuta na wahalar da mutanen Jumhuriyar Nijar da dama, saboda haka sanarwar da majalisar ministocin kasar ta bada na cewa za’a rage masu kudin da suke biya muddin basu wuce anfani da kilowatts hamsin ba, ya faranta musu ciki matuka.

Wani daqn kasar, Malam Safiyanu, yace matsayin ministocin abin farin ciki ne garesu kuma su talakawa suna goyon bayan a yi hakan.

Jama’ar kasar da lamarin ya shafa zasu fara soma cin gajiyar ragwamen ne daga ranar daya ga watan daya na shekara mai zuwa, wato 2018.

Yayinda masu karamin karfi zasu samu rangwame su kuwa manyan kamfanoni nauyin biyan kudin lantarkin ne zai koma kansu.

Ga rahoton Haruna Bako da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Zata Ragewa ‘Yan Kasar Kudin Wutar Lantarki