Gwamnatin Nijar Tayi Shiri Na Musamman Domin Ambaliyar Ruwa

Tambarin Jamhuriyar Nijar

Biyo bayan harsashen da masana yanayi suka yi cewa daminar bana a jamhuriyar Nijar zata zo da ambaliyar ruwa a wasu wurare dalili ke nan da gwamnatin kasar ta yi shiri na musamman kafin lokacin.

Tun watan Maris na wannan shekarar gwamnatin kasar ta yi kundi ko shiri na musamman da zai tunkari duk matsalolin da ka iya faruwa sanadiyar ambaliyar ruwa. Misali, akwai tanadi na aikin agaji saboda annoba ko ashin abinci da dai sauransu.

An yi harsashen cewa ambaliyar ruwa zai shafi mutane kimanin dubu dari da arba’in da biyar, wato tamkar iyalai dubu goma sha biyar ke nan.

Cikin watan jiya gwamnatin kasar Nijar ta ajiye kayan da za'a bukata a sassa daban daban na kasar domin shirin ko ta kwana. Da zara wani abu ya faru a koina ba tare da bata lokaci ba sai a kai doki ko agaji. Kasar ta kafa kwamitoci koina da suke kula da wuraren da aka basu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Tayi Shiri Na Musamman Domin Ambaliyar Ruwa - 2' 10"