Gwamnatin Nijar Ta Taya Amurka Murnar Gudanar da Zaben Kasa

Shugaban Nijar Muhammadou Issoufou

Gwamnatin kasar Nijar ta taya Amurka da amurkawa murnar gudanar da zaben shugaban kasa tare da samun sabon shugaban kasa wanda yanzu yake jiran gado

Sakamakon zaben ya zo lokacin da ake jiranshi kuma amurkawa sun zabi wanda suka ga ya dace ya shugabancesu.

Zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali kuma ya ba amurkawa damar su zabi shugabansu. Yanzu da yake Donald Trump ne ya ci nasara Nijar na yiwa Amurka barka saboda 'yan Amurka sun kara jaddada dimokradiya.

Har lokacin da aka fara zaben babu tabbacin wanda zai ci domin Trump da Clinton suna kunne doki ne a ra'ayin masu jefa kuri'a.

Gwamnatin ta yi fatan zasu cigaba da yin hulda irin ta diflomasiya tare da samun taimakon da kasar ke ba Nijar akan yaki da ta'adanci. Suna cikin Nijar suna taimakawa ta yaki da ta'adanci, ta fannin labaru da fannin tattalin arziki.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Ta Taya Amurka Murnar Gudanar da Zaben Kasa - 2' 21"