Ita sabuwar gwamnatin ta kunshi membobi arba'in da biyu da yanzu suka kama aiki a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadou Issoufou tare da Firayim Ministan dinshi Brigi Rafini.
Shi dai Firayim Ministan shi ne ya gabatar da kasafin kudin tare da tsare-tsaren ayyukan da gwamnatin zata yiwa al'ummar kasar nan da shekaru biyar masu zuwa.
Firayim Ministan yace za'a kashewa fannin tsaro kashi goma cikin dari na kudaden, yayinda fannin ilimi ke da kashi ishirin da biyar. Shi ma fannin kiwon lafiya nada kashi goma.
Ayyukan cigaban karkara da samarda cimaka zasu kwashi kashi goma sha biyar. Fannin samarda ruwan sha nada kashi tara. Sannan fannin makamashi da ayyukan gine gine nada kashi goma. Sauran fannonin nada kashi ishirin da daya.
Tsarin da gwamnatin Brigi Rafini ya gabatar ya samu karbuwa daga 'yan majalisun kasa da kuri'u dari da goma sha takwas daga cikin dari da saba'in da daya. Sai dai 'yan adawa ko sauraren gwamnatin basu yi ba balanatana ma su amince da shirin. Daga baya ma ficewa suka yi daga zauren majalisar.
Alhaji Murtala Mamuda dan majalisa ne na bangaren adawa yace gwamnati ta taka dokar kasa saboda akwai bangaren mata da ya kamata a basu amma ba'a basu ba. Yace saboda karancin kudi bai kamata a ce kasar ta nada ministoci arba'in da biyu ba. Yace ba daidai ba ne a ce akwai 'yan majalisa gidan kaso da yanzu suka kwashe fiye da watanni uku a tsare amma ba'a waiwayesu ba.
Amma masu rinjaye sun kwatanta maganar 'yan adawan da rashin abun fada. Alhaji Shafi'u Magarya dan majalisa na bangaren masu rinjaye yace 'yan kasa sun riga sun san an yi masu aiki, kuma aikin na gama gari ne ba na wuraren da aka zabi jam'iyyar dake mulki ba kadai. Yace kunya ce 'yan adawa ke ji, a ce yau sun rasa abun da zasu fadi. Yace da sun zauna a majalisar da sun ga tonon asiri.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5