Gwamnatin Nijar Ta Dauki Matakan Dakile Satar Jarabawar Kammala Ilimin Sakandare

Tambarin Jamhuriyar Nijar

Satar jarabawar kammala karatun ilimin sakandare a jamhuriyar Nijar na neman zama ruwan dare gama gari domin ko 'yan watannin da suka gabata sai da satar jarabawar masu koyan aikin jinya ta jawo cecekuce domin samun hannun wasu manya a lamarin

A 'yan shekarun nan satar jarabawa ta yi kamari a jamhuriyar Nijar musamman a manyan birane inda wasu 'ya'yan manya da na attajirai ke anfani da gatanci domin cin jarabawa ta kofar baya.

Dalili ke nan hukumomin ilimin kasar suka gayyaci hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta shigo cikin lamarin domin takawa masu wannan mummunar dabi'a birki.

Muhammad Maidashi daraktan ma'aikatar jarabawa dake ofishin ministan makarantun sakandare yace kowa ya san da cewa manya da masu hannu da shuni sun mayar da jarabawar kammala karatun sakandare tamkar wani abun da zaka shiga kanti ka biya kudinka ka dauka. Yace ana sayar da takardar kammala karatun. Inji shi idan mutum nada kudi sai ya je inda ake cuwacuwa ya biya dansa ya samu takardar. Yace idan gwamnati ta bari aka cigaba da haka to za'a karya ilimi.

Maidashi yace yau shekaru uku ke nan da aka shiga yaki da wannan muguwar dabi'a. Yace ta kai har wanda bashi da kudin biya sai a fidda dansa.

Domin tabbatar da wannan shirin dakile satar jarabawa na hadin gwuiwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa tuni ta aika jami'an leken asiri a cibiyoyin jarabawa na jihohi daban daban. Mataimakin daraktan hukumar Salihu Ubandoma, yace suna da jami'ansu da zasu baza duk inda ake jarabawar. Yace babu mamaki a kama mutane a kowace cibiya ko a cikin dalibai ma.

Kungiyoyin malaman makarantu sun yi na'am da matakan magance cuwacuwa a jarabawar sakandare ta wannan shekarar. Yusufu Arzika shugaban kawancen kungiyoyin malaman makarantu yace babbar cuwacuwa ta samo asali ne daga gwamnati wadda ta rage fannonin da dalibi ya kamata ya ci daga goma zuwa bakwai.

Ana fara jarabawar ta bana ne yayinda kungiyoyin malamai suka kira magoya bayansu da 'yan kugiyoyinsu da su kauracewa jarabawar domin gwamnati ta gaza biyan malaman makaranta dake aikin kwantiragi albashinsu na akalla watanni uku.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Ta Dauki Matakan Dakile Satar Jarabawar Kammala Ilimin Sakandare - 3' 03'