Kamfanonin da gwamnatin Nijar tace ta baiwa lasisin hakan ma'adanai sun hada da kamfani mai cibiya a Swaziland, da na kasar Turkiya da Gabal dake Yamai da wani kamfanin Nijar da zai gudanar da binciki hako karfen uranium a yankin Agadez.
A karkashin yarjeniyoyin da ta yi da kamfanonin kowannensu ya dauki alkawari mutunta dokokin tafiyar da harkokin ma'adanan kasar. Misali, biyan haraji, samar da aikin yi ga 'yan kasa, daukan matakan inganta rayuwar mutanen da ake hako ma'adanan a yankinsu domin samar da cigaban karkara na cikin dokokin da zasu kiyaye.
Wasu cikin kamfunan sun amincewa gwamnatin Nijar ta saka jari cikinsu domin damawa da 'yan kasar ta hannun jarin da gwamnati ta saka.
Kungiyar dake fafutikan ganin an yi haske da adalci wajen tafiyar da sha'anin ma'adanan karkashin kasa ta gargadi gwamnatin Nijar ta yi takatsantsan.
Audu Mamman Loko shugaban kungiyar dake fafutikan an yi adalci yace akwai kamfanonin kasashen waje dake zuwa kasar Nijar saboda yaudara. Yana mai cewa suna zuwa su ce zasu saka jari, zasu dauki 'yan kasa aiki, amma da zara an fara sai su bace, wasu ma su ki yin aikin gaba daya. Yace duk wanda gwamnati zata ba izini yakamata 'yan kasa su sani, su kuma san wanda aka ba.
Jami'an fafutika sun ce dagewa akan mutunta dokokin Nijar ya zama wajibi. Suna cewa a shirye suke su goyi bayan gwamnanti akan wannan lamarin kuma su shaidawa jama'a.
Jamhuriyar Nijar na cikin kasashen duniya ma fi arzikin karfen uranium. Sai dai 'yan kasar ba sa cin moriyar wannan arzikin da Allah ya basu. Misali, kamfanin Areva na kasar Faransa ya yi shekaru 40 yana hakan uranium a Nijar araha banza. Dalili ke nan da kungiyoyi a shekarar 2016 suka matsawa gwamnati lamba ta kafa dokokin kare ma'adananta.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5