Gwamnatin Nijar ta bai 'yan gudun hijirar Najeriya da wasu kasashe 860 cikakkun takardun izinin zama a cikin kasar cikin 'yanci da walwala duk kuma da matakin da gwamnatin Nijar ta dauka na haramta wa 'yan kasashen ketare shiga kasar ba tare da takardu ba.
Wannan dai shi zai kawo karshen jiran tsammani ga yan gudun hijira sama da dubu biyu da suka shafe shekaru a sansanin yan gudun hijira dake jira a Agadas da ke arewacin.
Basu wadannan takardun ya biyo bayan wani zama na tantance takardun su da kwamitin da ke da alhakin tantance takardun 'yan gudun hijira, inda kwamitin ya amince da bukatar a bai wa yan gudun hijira da suka fito daga Najeriya da kuma Sudan 860 takardun damar zama kasar cikin yanci da walwala. Maman Laye Ibrahim, Darektan ma’aikatar kula da takardu da yan gudun hijira.
'Yan gudun hijirar da suka samu wannan matsayin daga gwamnatin Nijar sun kasance a cikin rukunin yan gudun hijirar da makomar su a kasashen su na asali ke tattare da rashin tabbas Nasiru Salihu wani yan gudun hira ne da ya fito daga Zamfara yana daga cikin wadanda aka bai wa takardun.
Wasu yan gudun hijirar da basu mallaki takardun ba sun soki yadda ake jan kafa wajen tantance takardun su. Jean Bimako, wani dan gudun hijira daga Afirka ta tsakiya cewa yayi, "Mun kosa game da yadda tsarin tantancewa ke gudana. Yau mun shafe tsawan lokaci anan. A halin da mu ke a yanzu tamkar bamu da wata kasa ne. Mu na kira ga gwamnatin Nijar da masu tallafawa da su gaggauta samar mana da mafita duba da irin yanayin rayuwa da muka shiga."
Yanzu haka dai kwamitin zai ci gaba da nazartar wasu karin yan gudun hijira da za a bai wa takardu. Wannan dai na zuwa ne bayan da a watan da ya gabata gwamnatin Nijar ta sanar da haramta wa yan kasashen ketare shiga kasar ba tare da sun mallaki wasu takardu ba
Kasar Nijar dai yanzu haka na karbar dubban 'yan gudun hijira daga kasashen Afirka da na Asiya wanda ta rarraba a cikin jihohi biyar na kasar ciki har da jihar Agadas.
Saurari cikakken rahoton
Your browser doesn’t support HTML5
Nijar Ta Ba Baki Takardu.mp3