Gwamnatin Neja Zata Kafa Makarantar Horas da Aikin Ngozoma

Jami'an kiwon lafiya

Sabili da rage mace-macen mata lokacin da suka zo haihuwa gwamnatin jihar Neja zata kafa makarantar horas da aikin ngozoma a garin Kontagora

Gwamnatin jihar Neja ta fara aikin samar da wata makarantar koyas da aikin ngozoma a garin Kontagora.

Kafa makarantar na daya daga cikin matakan da gwamnatin ke dauka na samar da kwararrun ngozomomi domin rage yawaitar mace-macen mata wajen haihuwa musamman a yankin Kontagora.

Dr Muhammed Bashar kwamishanan ma'aikatar ilimi mai zurfi na jihar yace malaman kiwon lafiya basu wadata a koina ba. Samun irin wadannan makarantun zai taimaka wurin kula da kiwon lafiyar mata musamman lokacin da suka zo haihuwa. Zai kare lafiyar jarirai ya kuma rage hatsarori da yanzu ake fuskanta a asibitocin jihar. Dalili ke nan da gwamnati ta dauki aniyar kafa makarantar a Kontagora domin a wannan yankin babu irin makarantar.

Tuni aka fara gina makarantar. Ya yabawa sarkin Kontagora wanda ya ba gwamnatin kasa fiye da hekta tara kyauta. Bugu da kari ya gina azuzuwa guda hudu manya-manya. Ganin haka gwamnati ta saka nera miliyan goma akan aikin makarantar. Ban da haka gwamnati ta kara bada karin nera miliyan talatin.

Al'ummar yankin Kontagora sun ce sun yi maraba da matakin domin wani cigaba ne ta fannin kula da lafiyar yankin.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Neja Zata Kafa Makarantar Koyas da Aikin Ngozoma - 2' 55"