A kokarin kawar da ayyukan ta'addanci a jihar Neja, gwamnatin jihar ta baiwa 'yan bangan jihar gudummawar motoci kiran hilux guda 18 domin yaki da 'yan ta'adda a garuruwa da kauyukan karkara.
Cikin 'yan kwanakin nan jihar tana fuskantar hare haren dake hallaka jama'a a wasu kananan hukumomi.Na baya bayan nan shi ne kisan gillar da aka yiwa wasu mutane 26 cikinsu har da wasu mutane bakwai da aka yiwa yankan rago a masallaci a kauyen Ibogi dake yankin Mokwa.
Onarebul Zakari Jikan Toro kwamishanan ma'aikatar kananan hukumomi da masarautun jihar yana mai cewa tunda aka tarwatsa 'yan Boko Haram daga dajin Sambisa 'yan ta'addan na nemi mafaka a wasu wuraren dake zaman lafiya. Yace su ne suke gangarowa zuwa jiha irin Neja. Kwanan nan sun lura wasu tsiraru suna tada hanakali. Dalili ke nan da gwamnati ta zabura ta jawo hankulan 'yan banaga da jami'an tsaro da su tashi tsaye su shawo kan matsalar.
Shi ma Onarebul Gambo Tanko Kagara shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar Neja yace taimakawa 'yan bangan zai taimaka kwarai wajen inganta tsaro. Yan ta'addan suna yawan sace mutane maza da mata tare da yiwa mata fyade don haka 'yan bangan zasu iya zagayawa koina.
Wasu cikin 'yan bangan ma sun furta albarkacin bakinsu akan gudummawar da suka samu..Sun sha alwashin kare kasarsu su tabbatar babu ayyukan ta'addanci koina
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5