Daruruwan gidaje ne gwamnatin jihar Neja ta amince da rushesu a ungiwar tsohon barikin sojoji dake Suleja da yanzu sojojin suka tashi.
Mazauna unguwar sun ce yau da safiyar Litinin motar rushe gidaje ta yi masu dirar mikiya tare da rakiyar jami'an tsaro inda ta cigaba da rushe gidajen jama'a.
Wadanda lamarin ya shafa sun ce suna cikin wani yanayi na rudani. An ba mutanen takardar gargadin ficewa daga gidajen amma sun ce wai na bakin hanya aka fada masu. An basu kwana uku ne kafin a soma rushe gidajen.
Kodayake wasu sun tattara kayansu kafin a rushe gidajen nasu basu san halin da suke ciki ba ko inda suka nufa yanzu.
Malam Aliyu Jibril Bisallah jamiin hulda da jama'a na karamar hukumar Suleja yace gwamnati ta dauki matakin ne domin ta karbe filinta wanda tun asali aro aka baiwa sojoji tun wajejen shekarar 1970. A yanzu sojojin sun tashi kuma wadanda suka mamaye filin ne ake kora.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5