Gwamnatin ta fitar da ofishin mataimakin gwamnan daga harabar gidan gwamnatin jihar zuwa wani wuri daban.
Wannan wata alama ce da ta nuna dangantaka na kara yin tsamari tsakanin gwamna Dr Muazu Babangida Aliyu da mataimakinsa Alhaji Ahmed Musa Ibeto. Shi dai mataimakin ya canza sheka daga jam'iyyar gwamnati ta PDP zuwa jam'iyyar adawa ta APC.
Kodayake gwamnatin jihar tace ta dauki matakin ne saboda gyaran da ake son a yiwa ofishin, amma magoya bayan mataimakin sun ce lamarin ba haka yake ba. Shehu Ibrahim Kagara na hannun daman mataimakin gwamnan yace ba wani dalili ba ne illa kataddamar dake tsakanin gwamnan da mataimakinsa. Idan da aiki lamarin ya shafa da sai a bi doka.
Yanzu wurin da aka ba mataimakin babu ruwa babu wuta. To amma gwamnatin ta hakikance bata da wata manufa saidai na yin kwaskwarima ga ofishin kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Idris Ndako ya sanar.
Tun daga lokacin da ya fice daga PDP mataimakin gwamnan ya sha yin korafe korafe kama daga rage jami'an tsaronsa da kuma hanashi shiga taron majalisar zartaswar jihar.Bugu da kari gwamnan ya mika ragamar mulkin jihar ga shugaban makalisar dokoki yayin da zashi ummra.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5