A kwanakin baya ne gwamnati ta soke takardun sayan kujerun zuwa hajji da ma'akatar alhazan jihar ta sayarwa jama'a.
Saboda wannan matakin ya sa ta kafa wani kwamiti na musamman da zai tafiyar da harkokin ma'aikatar.
Alhaji Idris Azozo kwamishanan ma'aikatar ruwa ta jihar shi ne shugaban kwamitin dake kula da ma'akatar alhazan da gwamnati ta kafa.
Yace da suka zo domin su gano irin barnar da aka yi sun yi nazarin abun da za'a yi a kawar da cuwa-cuwar a kuma tabbata ba'a cigaba da yin hakan ba. Misali yace gwamnati tace a ba duk wanda yake son zuwa aikin hajji takarda ya kuma biya nera dubu biyar sai suka samu labari ana saidawa dubu dari har zuwa dubu dari biyu.
Kawo yanzu sabon kwamitin ya kusa gama sayar da takardun akan kudin da gwamnati ta kayyade.
Ita ma hukumar alhazan Najeriya ta baiwa hukumar jihar kudi sama da miliyan talatin da daya da za'a rabawa alhazan jihar da suka yi aikin hajjin bara.
Mukaddashin sakataren hukumar alahazan Alhaji Umar Maku Lapai ya yi karin haske akan kudaden.Yace an dawo masu da kudaden ne saboda wasu ayyuka da ba'a yiwa alhazan ba.
Alhaji Tanko Kagara shugaban kananan hukumomi da aka ba alhakin raba kudin yace idan zasu biya zasu yi anfani da shugabannin kowace karamar hukuma tare da sarakunan gargajiya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5