Takun sakar ta samo asali ne daga tara kudaden fansho da 'yan kwadagon suka ce ana jire masu daga cikin albashinsu amma kuma ba'a kaisu inda ya kamata.
Ma'aikatan gwamnatin jihar sun ce tun shakarar 2007 aka fara cire masu kashi goma sha biyar daga cikin albashinsu kowane wata a matsayin kudin fansho. Kungiyar kwadagon tace kawo yanzu basu gane ko sanin inda ake shiga da kudaden ba.
A wani taron manema labarai shugaban kungiyar kwadagon reshen jihar Neja Kwamared Idris Ndako yace duk da binciken da suka gudanar akan kudaden har yanzu basu gane bakin zaren ba. Yace bukatarsu yanzu ita ce dakatar da cire masu kudi da ake yi domin illar dake tafe da cigaba da cire masu kudi. Illar ko ita ce ma'aikata basa samun tuntuba cewa an cire masu kudaden kuma ga inda suka shiga. Sabili da haka ma'aikata sun damu.
Shi ma shugaban kwadago na TUC a jihar Kwamred Yunusa Tanimu yayi karin haske akan matsalar. Yace kudi ne da ake cirewa ana tarawa domin ranar da ma'aikaci zai bar aiki ya samu abun dogaro a kai. To sai yanzu an ce kudaden nada matsala dalili ke nan suka koka. Ba'a biyan kudadencikin asusun ritaya na kowane ma'aikaci kamar yadda doka ta tanada.
'Yan kwadagon sun lura cewa ba'a bin dokokin da aka tsara dangane da cire kudin fansho da inda za'a kaisu. Kudin ana ciresu amma ba'a kaisu inda ya kamata -inji Tanimu.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5