A taron manema labarai domin fayyace yadda gwamnatin ta kashe kudin Paris Club da gwamnatin Buhari ta rabawa jihohi, kwamishanan kudin jihar Mr. Dominic Bako yace jihar ta samu Nera biliyan takwas da digo hudu ne.
Kwamishanan ya kara da cewa cikin kudin kashi 64 mallakar gwamnatin jiha ne yayinda kashi 36 na kananan hukumom ne.
Inji Mr Bako tun farko Shugaba Buhari ya ba gwamnoni umurnin su ware kashi hamsin na kudin domin biyan albashi da fansho, sauran kashi hamsin din kuma su gudanar da ayyukan inganta rayuwar al'ummominsu.
Dangane da albashi kwamishanan yace ma'aikatan jihar basa bin gwamnati bashi. Albashin watanni biyu da suke korafi a kai na watannin Yuli da Agustan bara ne lokacin da suke yajin aiki. Yace wadanda suka yi aiki a lokacin an riga an biyasu hakkokinsu.
Bisa ga jin tausayi gwamnan jihar yayi alkawarin biyan wadanda basu je aiki ba a lokacin yajin aikin a duk lokacin da alamura suka daidaita.
To saidai shugaban kungiyar kwadagon jihar Abdullahi Adeka yace iyakacin saninsu gwamnati ta biyasu har zuwa watan Disamban bara ne amma akwai wasu watanni da basu karkare ba. Yace akwai gibi a albashin watannin Satumba da Oktoba da Nuwamban bara. Bisa ga yarjejeniyar da suka yi gwamnati ta yadda ta cike gibin watan daga ragowar kudin Paris Club.
Shi ko shugaban hadaddiyar kungiyar dake shiga tsakanin ma'aikatan da gwamnatin Nasarawa Sule Usman yayi bayani akan albashin kananan hukumomi. Yace suna bin albashin wajen watanni tara da har yanzu ba'a biyasu kakaf ba. Yace suna bin gwamnati domin a biya kudaden lami lafiya.
Kwamishanan kananan hukumomi Tijjani Aliyu Ahmed yace suna biya amma bai kai kimanin abun da ya kamata a biyasu ba saboda raguwar kudaden dake shigowa. Tunda tattalin arziki ya tabarbare wajibi ne kowane bangaren rayuwa ya samu matsala,inji kwamishanan. Yace a kudin Paris Club an ba kananan hukumomi Nera biliyan ukku amma shigaban kasa ya roka a yi anfani da rabin kudin a yiwa al'umma aikin inganta rayuwarsu.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5