Gwamnatin tarayyar Najeriya da jami'an tsaron kasar sun sha alwashin daukan sabbin matakan durkushe duk wani yunkurin samame da kungiyar Boko Haram zata shirya yi a kowane sashen kasar.
Ministan tsaro Janar Mansur Dan Ali mai ritaya shi ya bayyanawa Muryar Amurka hakan biyo bayan harin ba zata da kungiyar Boko Haram ta kai Maiduguri jiya.
Ministan yana mai cewa kowane lokaci 'yan ta'addan na neman suyi farfagandar nuwa duniya har yanzu akwaisu. Yace farmakin da suka kai na bazata ne kuma yana iya faruwa koyaushe amma idan mutane suna tseguntawa jami'an tsaro abubuwan dake faruwa nan da nan za'a katsesu.
Dangane da farmakin jiya ministan yace nan take aka gama dasu. Babu wanda ya samu shiga birnin Maidugurin. Yace babu yadda za'a yi a samu jami'an tsaro koina. Amma mutanen dake wurin su ne zasu dinga taimakawa da bayanai da.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5