Gwamnatin Najeriya Za Ta Kafa Rundunar Yaki Da Satar Kadarorin Lantarki- Minista

Jami'an Civil Defense

Jami'an Civil Defense

Nasarar da askarawan yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ta samu ce tayi tasiri wajen yanke shawarar kafa irinta a bangaren lantarkin

Najeriya ta yanke shawarar kafa rundunar musamman da nufin kare turaku da kayayyakin lantarkinta.

“Mun yanke shawara tare da ministan lantarki a kan samar da rundunar da muka sanyawa suna “askarawan lantarki,” kamar yadda ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana lokacin da ya bayyana a shirin tashar talabijin ta Channels na hantsi mai suna Sunrise Daily na yau Juma’a.

Nigerian Interior Minister

Nigerian Interior Minister

Za a kirkiri askarawan lantarkin ne daga cikin jami’an hukumar tsaron farar hula ta “Civil Defense” kuma ita zata dauki gabarar yaki da satar kayan lantarki dake yawan janyo daukewar wuta a fadin kasar.

Nasarar da askarawan yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ta samu ce tayi tasiri wajen yanke shawarar kafa irinta a bangaren lantarkin.