Gwamnati ta dauki wannan matakin ne don dakile tasirin cire tallafin man fetur da ya kara uzzura tsadar rayuwa a kasar mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.
Sanarwar da ofishin mataimakin shugaban kasar ya fitar ta ce za'a raba hatsi da takin ne ta babban bankin kasar, kuma gwamnonin jihohi sun goyi bayan shirin. Ba ta ba da cikakken bayani kan matakan ba.
A makon da ya gabata ne dai majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya don taimakawa wajen magance wahalhalun da tashin farashin man fetur ya haifar bayan dakatar da tallafin man fetur a watan Mayu.
A ranar Talata farashin Man Fetur a Najeriya ya kai Naira 617 ($0.78) a kowace lita.
Gwamnati ta yi kudurin fito da tsarin jigilar zirga-zirgan jama'a ta motoci masu amfani da iskar gas tare da kafa masana'antar canza gas da motocin bas masu amfani da wutar lantarki a duk fadin kasar.
Tinubu ya fara sauye-sauye mafi girma a Najeriya cikin s.hekaru da dama domin tunkarar matsalolin da suka hada da dimbin basussuka.
Kungiyoyin kwadago sun soki yadda gwamnati ta kawo karshen tallafin man fetur ba tare da daukar matakan rage tashin farashin kayayyaki ba.
A cikin watan Yuni ne manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya tare da gwamnatin kasar suka sanya wa'adin makwanni takwas don kammala yarjejeniyar kara mafi karancin albashin ma'aikatan gwamnati.