Kungiyar kiwon lafiyar Najeriya zata kashe yawan kudi Naira miliyan 415 shekara mai zuwa domin kauda cutar kanjamau da zazzabin cizon sauro.
WASHINGTON D.C —
Kungiyar kiwon lafiyar Najeriya zata kashe yawan kudi Naira miliyan 415 shekara mai zuwa domin kauda cutar kanjamau da zazzabin cizon sauro.
Wannan tanaji yana cikin kasafin shekara ta 2014, wanda Shugaban Kasa Godluck Jonathan ya shinfida gaban ‘yan majalisar kasa ta wurin ministan kudi, Ngozi Okonji-Iweala.
Domin shekara ta 2014, gwamnatin tarayya ta tanadawa ma’aikatar lafiya kimanin Naira biliyan 15.497. Daga cikin wannan, an shirya yin amfani da Naira biliyan 9.109 domin manyan ayyuka da kuma biliyon N6.387 domin gudanarwa ta yau da kullum.
Cikakken bayanini wannan kasafin ya nuna Naira miliyan 115 zai kare kan kawar da cutar kanjamau; Naira miliyan 213.321 kan kawar da cutar kansa da kuma sauran Naira miliyan 85.653 kan zazzabin cizon sauro.
Bisa ga wannan tsari, ayyukan maaikata da suka shafi yaki da kanjamau sun hada ne da fadada bayas da magunguna, kulawa da kuma tallafawa wadanda ke dauke da kwayar cutar; kafa da kuma inganta wuraren aiki kan kanjamau guda dari da kuma samas da kayan gwajin HIV.
Abubuwan da yaki da zazzabin cizon sauro ya kunsa kuma akwai shirye shirye kamar su; kudaden da za’a kashe wajen rarraba gidajen sauro mai magani da kuma sauran magunguna sauro; kuma kan kawar da kansa kasafin ya hada da binciken nawayar da kasar take da shi na kansa, yin amfani da na’urorin maganin kansa a ma’aikatun lafiya na kasa, sayen kayayyakin gwaji wadanda za’a iya yawo da su da kuma goyawa maganin kansa baya a manyan asibotocin kasar nan.
Wani Karin haske a kan kasafin kudin ya nuna cewa maaikatar ta ajiye ware Naira biliyan 9.109 domin gine-gine /tanajin asibitoci/ maaikatun lafiya.
Tsarin rabon kudin ya nuna cewa maaikatar ta kirkiro wasu sabbin shirye shirye da suka hada da sayen magunguna masu bugaswa wanda zai ci Naira miliyan 32.6; kididdigar yanayin lafiya, Naira miliyan 55.264; tsarin lafiya na tashoshin jiragen ruwa, Naira miliyan 50.356; kayyade da kawarda cututtuka, Naira miliyan 88.224; tallafi domin maaikatan lafiya da shirin unguwar zoma, Naira miliyan 246.869; aiwatar da shirin lafiya na wayar iska, Naira miliyan 80.708; da sauransu.
Wadannan basu hada da Naira miliyan 107.754 wadanda aka kebe domin sayen Fetur da sauransu; miliyan N 44.32 domin tattaunawa da kuma hayar masana; Naira miliyan 24.359 domin horaswa; Naira miliyan 138.289 domin Sayen kayan office; Naira miliyan 188.5domin tafiye tafiye, Naira miliyan 18 domin wutar lantarki da kuma Naira miliyan 4.7 domin kudaden tarho.