Gwamnatin Najeriya Ta Wanke Jami’in Binance Gambaryan Daga Dukkanin Tuhuma

  • VOA Hausa

Tigran Gambaryan, hagu, da lauyansa

Lauyan hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya, ne ya sanar da janye tuhume-tuhumen a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya dake abuja.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da take yiwa babban jami’in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan a bisa dalilai na rashin lafiya.

Gambaryan ya kasance a tsare yana fuskantar shari’a akan halasta kudaden haram tun cikin watan Afrilun da ya gabata.

Lauyan hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya, ne ya sanar da janye tuhume-tuhumen a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya dake abuja.

Hakan ta faru ne kwanaki 2 kafin cikar wa’adin 25 ga watan Oktoban da muke ciki da alkalin ya ajiye domin cigaba da sauraren karar a juma’ar data gabata.

Da yake janye tuhume-tuhumen, lauyan efcc yace Mr. Gambaryan, dan kasar Amurka kuma ma’aikatan Binance, na fuskantar tuhuma ne kawai saboda abinda kamfaninsa ya aikata.

Lauyan Gambaryan, Mark Mordi, ya amince da kalaman lauyan masu kara, inda yace wanda yake karewa ba shi da ra’ayi a manyan shawarwarin da suka shafi kudi da kamfanin ke yankewa.