A kokarin kawo karshen tsananin karancin man fetur dake faruwa yanzu a Najeriya, gwamnati ta baiwa ministan man fetur umurnin tabbatar da yawaitar man a duk fadin kasar cikin dan kankanin lokaci.
Kafin umurnin, 'yan kasar sun fara kokawa akan tsananin karancin man da suke fuskanta wanda ya kusa durkushe harkokin tattalin arziki da rayuwar al'umma duk da cewa wai akwai man, wasu ne suke karkatashi suna boyewa.
Liman Katari, daya daga cikin shugabannin kungiyar hadin kawunan Musulmi da Kiristoci a Najeriya, ya bayyana irin koke-koken mutane sanadiyar karancin man, abun da shi kansa ya fuskanta.
Injishi, jama'a suna wahala. Ya ce kafin su shiga Abuja daga Kaduna sai da suka kwashe awa hudu. Sun shiga layin mai a Jere sun yi kusan awa biyu kafin a gaya masu man ya kare. Ko a Abuja ma sai da suka yi awa biyu a layi kafin su samu mai.
Liman Katari na ganin rashin yawaitar man ka iya shafar tattalin arziki saboda da man wani zai tayar da janareto ya yi aikin da zai samu abincin ranar. Da man ne talaka yake samun abun yi ba sai ya dogara ga gwamnati ba, inji Liman.
A kasuwar bayan fage, Liman Katari ya ce N300 ake sayar da lita daya ta man fetur wato kwatankwacin N1200 galan daya ke nan.
Dangane da batun karancin man da kuma umurnin da gwamnati ta bayar, Malam Garba Shehu, kakakin fadar shugaba Muhammad Buhari, ya ce tun farko gwamnati ta yi tanadin man isasshe domin gujewa aukuwar karanci. A cewarsa duk lokacin da aka kawo karshen shekara wasu kan shiga harkokin mai domin su ci kazamar riba tare da gallazawa jama'a. Injishi domin dakile aukuwar karancin, sai gwwamnati ta ribanya adadin man da take shigowa dashi a wannan lokacin. Ya ce man "fetur yana nan a dankare a tanki tanki da kuma jiragen ruwa. Babu wani dalili na rashin mai idan ba don rashin adalci da tausayi ba na dan Adam akan dan Adam"
Yanzu dai gwamnati, ta bakin Malam Shehu Garba, ta na tura jami'an tsaro kuma duk wanda aka kama yana boye mai za'a kwace a sayar wa jama'a a kuma yi masa hukunci. Idan gidan mai ne ma ana iya kwace lasisin aikinsa. Baicin hakan ana kara baza tankunan mai domin ya yawaita a duk fadin kasar.
Ga rahoton Umar Faruk da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5