Gwamnatin Najeriya Ta Tura Dalibai 179 Zuwa Kasar Rasha Domin Karin Ilimi

Wasu dalibai

A wani mataki na habbaka harkokin ilimi a Najeriya, gwamnatin kasar ta bada tallafin karatu wa dalibai 179 don zuwa kasar Rasha karo Ilimi, matakin ya biyo bayan shirin karkashin yarjejeniyar ilimi tsakanin kasashen.

Daliban ilimin za su sami cikakken tallafi daga gwamnati wanda hakan zai ba su damar karatun digiri na biyu domin fadada ilimi karkashin tsarin zangon 2023/2024

Wannan yunƙurin na nuna himma da gwamnati ke yi wajen haɓaka haɗin gwiwar ilimi na duniya da ƙarfafa tallafinta ga ilimi. Yayin da waɗanda suka ci gajiyar shirin ke shirin tashi zuwa Rasha, ana sa ran cewa ƙoƙarinsu na ilimi zai ba da gudummawa mai ma'ana ga ci gaban kansu da kuma fa'idar ilimi.

A yayin taron da aka shirya wanda ya gudana a Abuja kafin daliban su dau hanyar su zuwa kasar Rasha, Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya yi jawabi ga daliban ilimin, inda ya bukace su da su zama jakadun kasarsu na kwarai a kasashen waje.

Farfesa Mamman ya jaddada masu cewa zabensu da aka yi ya biyo bayan tsare tsaren gwamnati da take yi na ajanda mai taken ‘sabuntawa’ wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta. Wannan ajanda na neman karfafawa 'yan Najeriya masu hazaka, kokarin ilimi da nuna kwarewa a muhimman fannonin ci gaban Najeriya.

Da ta ke wakilcin Ministan, daraktar ilimin manyan makarantu a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Hajiya Rakiya Gambo Iliyasu, ta jaddada muhimmancin kiyaye dabi’u da kuma mai da hankali kan karatu. Ministan ya yi gargadin a kan kallon wannan tallafin a matsayin wata dama da mutum zai yi yadda yaga dama, yana mai jaddada cewa damar da aka basu na nufin su karo ilimi kuma su dawo Najeriya don bada gudunmawa ga kasa da cigaba na musamman.

Da yake magana a madadin daliban, Moses Inalegu ya nuna godiya ga gwamnatin tarayya. Ya kuma tabbatar da aniyar su na ganin sun yi karatu haikan bisa tsari da inganci kuma sunyi alwashin baza su bada kunya ba.

Dakta Isa Abdullahi Kashere, malami a Jami’ar Tarayya da Kashere, ya yi wa muryar Amurka karin haske game da muhimmancin irin wannan tallafin ilimi ga cigaban kasa, Dakta Abdullahi yace hakika karo ilimi a kasashen da suka cigaba irin Amurka, China, Rasha da sauransu abu ne mai alfanu sosai ga kasashe masu tasowa irin Najeriya, musaman idan akayi la’akari da yawancin bangarorin da ake zuwa koyowa a wadannan kasashe bamu dasu a nan Najeriya ko kuma ma namu din ba wasu masu karfi bane, musamman ilimin da ya shafi kimiyya da fasaha na duniya irin su ilimin na’ura mai basirar dan adam, ilimin sararin samaniya da sauransu.

Da yake bayani game da hangensa na kalubalen da kan iya tasowa lura da rikicin da ke cigaba da barkewa na yaki tsakanin kasar Ukrain da Rasha, Dakta Abdullahi ya bayyana cewa baya tunanin daliban zasu fuskanci wanni babban kalubale na tsaro duk da cewa tattalin arzikin rasha ya dan ja baya kadan saboda takunkumin da manyan kasashen duniya suka kakaba mata, amma duk da haka babu wani dalibi da ya taba dawo Najeriya daga rasha saboda wani matsi sakamakon rikin, amma hakan ya sha faruwa ga dalibai ‘yan Najeriya da ke karatu a kasar Ukrain.

An yi kira ga daliban ilimi da su zama ‘yan kasa nagari, in sun isa kasar Rasha su maida hankali wajen karatun su, kuma kada ya kasance bayan sun kammala karatun yazama wata dama da za su guji kasarsu, a maimakon haka su dawo su bada gudunmawa koda na wani tsawon lokaci domin tabbatar da kawo cigaba wa Najeriya, duk da cewa dama hakan na cikin yarjejeniyar da suka sa hanu kafin suyi azama zuwa kasar Rashan.

Har ilayau, Ministan ya ci gaba da yi wa daliban ilimin jawabi a yayin wani taron tattaunawa da su tun kafin tashin jirgin, inda ya shawarce su da su ba da fifiko ga ci gaban Nijeriya idan sun kammala karatunsu. Da yake jaddada mahimmancin kyawawan dabi'u a matsayinsu na jakadan Najeriya, Farfesa Mamman ya taya wadanda aka karraman murna, inda ya jaddada irin jarin da Najeriya ta zuba a karatun nasu da fatan samun tasiri mai kyau bayan dawowar su.

Yayin da dalibai 179 ‘yan Najeriya suka nufi Rasha domin yin karatu, wannan ba tafiya ce ta kashin kai kadai ba, a’a alama ce ta jajircewar Najeriya wajen neman ilimin a duniya, wadannan daliban ilimi da suka samu tallafin karatu na Yarjejeniyar Ilimi tsakanin Najeriya da kasar Rasha, zun zama wakilai da jakadun Najeriya wajen nuna kyawawan halayya da bin dokokin kasa.

~ Yusuf Aminu Yusuf