Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce gwamnatin Najeriya ta tsorata da ziyarar da ya kai Amurka yana mai nuna cewa ziyarar ba ta masu dadi ba.
Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne a zamanin mulkin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai Sashen Hausa na Muryar Amurka a yau.
Yayin kuma wannan ziyara ta Atiku, rahotannin daga Najeriyar sun nuna cewa, gwamnatin kasar ta ce ba damuwarta ba ne idan Atiku ya je Amurka,
A lokacin da yake ganawa da manema labarai a yau, Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya ce abin da suke jira shi ne Atiku ya dawo ya zo ya amsa tambayoyi kan hannun da ake zargin yana da shi a durkushewar bankin kasar.
Wasu dama na ganin ziyarar ta Atiku a Amurka za ta kawo karshen tababar da aka jima ana yi ta cewa, ba zai iya zuwa Amurka ba, domin yana gudun hukumomi za su kama shi.
Kafafen yada labaran Amurka kuma sun yi nuni da cewa, da alamu gwamnatin Amurka ta yi na'am da dan takarar.
Amma a nasa bayanin, Atiku ya ce koda gwamnatin Amurka na goyon bayan wani dan takara, ba za ta taba nunawa a fili ba.