Gwamnatin shuga Muhammadu Buhari, karkashin jagorancin ministan kwadugo Sanata Chris Ngige, ya bayyanar da daya daga cikin alkawalin gwamnatin su, a lokacin yakin neman zabe, na cewar zasu samar da aikin yi ga mutanen Najeriya dubu dari biya 500,000. A lokacin da yake zantawa da manema labarai ministan, ya bayyanar da cewar kada mutane su dauka cewar aikin da zasu samar, zai fito ne kawai daga wajen gwamnati.
Ba haka abun yake ba, kokarin su shine su bama mutane horo da zasu iya dogaro da kansu, wajen sana’o’in hannu. Kokarin da gwamnatin su take yi shine, suga cewar kowace jiha zata iya biyan albashin ma’aikata, batare da an rage yawan suba. Za kuma su kashe kudi kimanin rabin naira tirilliyan daya, don koyama mata da masu naka milliyan takwas sana’o’i, sanao'i a kowane bangare.
Yan zu haka dai sunyi wani shiri na amfani da hukuma zabe ta kasa INEC, don samun sunayen mutane da suke a karkara. Kuma zasu yi la’akari da mata da mazajen su suka mutu, wajen karfafa su, su iya dogaro da kansu, haka suma matasa za’a basu wannan horas war a fannoni da dama. Suna kuma sa ran zasu fara da kashi talatin na kananan hukumomi dari bakwai da saba’in da hudu da ake da su a Najeriya a karon farko.
A bangare daya kuwa wasu ‘yan Najeriya naganin cewar ya kamata ace gwamnati, tayi kokarin duba wasu bagarorin da suka shafi rayuwar ‘yan kasa. Muhammad Alkali Sarki, wani mutun ne da yake murmurewa daga rikicin boko haram, yake kira da gwamnati tayi kokarin samar ma matasa aikinyi don ta haka ne kawai za’a iya gujema ire-iren aikin ta’addanci a tsakanin matsa.
Shi kuwa wani matashi Yusuf Lamido Cikaire, ya bayyanar da cewar basu gamsu da yadda gwamnatin take gudanar da tsarurukan su ba, domin kuwa yana ganin cewar a baya an kawo wadanda basu san komai ba, shi yasa kasar ta shiga cikin wani hali, don haka wannan wata damace da ya kamata su kawo masana kuma kwararru da zasu gudanar da aiki yadda ya kamata.
Your browser doesn’t support HTML5