Ministan Makamashin Najeriya, Injiniya Sale Mamman, ya ba da umurni nan take hukumar kula da farashin wuta ta NERC ta dakatar da karin farashin wutar da ta yi bisa dogaro da batun raguwar darajar kudi da lamuran tattalin arziki.
Injiniya Mamman ya ce yanzu za a koma kan teburin shawara da kungiyar kwadago don fitar da sabuwar matsaya, wadda kowa zai iya amanna da ita, kafin a dau wani mataki na daban idan ta kama.
Sanarwa daga Mai Taimaka wa Ministan Kan Hulda da Jama'a, Ado Adamu ta ce yanzu an koma tsarin da ake kai na baya a watan Disamban da ya gabata da ya janye duk wani kari kan wasu daga rukunoni biyar na masu amfani da wutar. Ado Adamu ya kara da cewa janye karin ya biyo bayan tsari na sauraron kukan da jama'a su ka yi ne.
Gabanin nan wani na hannun daman Ministan, Alhaji Idris Muhammed Madakin Jen, ya musanta shaida wani kari amma bisa katin sayen kudin wuta maimakon ya yi la'akari da yadda wutar ke shanyewa ne bayan sanya kati a mitar "iya kudinka, iya wutarka"
Tsohon Mai Kula da Shige da Fice a lokacin yakin neman zaben Shugaba Buhari, injiniya Magaji Muhammad Yaya, ya nuna takaicin yawan karin kudin wutar.
An kula cewa wutar lantarki na da tasiri ainun wajen rage kuncin tattakin arziki.
Ga Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Muhammadu Buhari, Nigeria, NERC, da Najeriya.