Gwamnatin Najeriya Ta Ce Ta Na Kokarin Murkushe 'Yan Bindiga

Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

Yayin da ake cigaba da koke-koke kan matsalar tsaro a Najeriya, inda 'yan bindiga iri-iri ke ta karkashe mutane, baya ga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, gwamnatin kasar ta ce ta dukufa wajen ganin bayan dukkan miyagu a kasar.

Garba Shehu ya ce Gwamnatin Najeriya na iya bakin korinta wajen ganin an shawo kan mastalar hare-haren yan bindiga da ta addabi wasu garuruwan arewacin Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da ya yi da Muryar Amurka inda ya ce “akwai bukatar a hada karfi wuri guda, gwamnati na iya bakin kokarinta anan Abuja, wajen samar da kayan aiki ga jami’an tsaro da suke sadaukar da ransu don kare al’umma.

Ya ce gwamnatocin jahohi, suma, ya kamata su shigo ciki don bada tasu gudunmawa, domin a samu a hada karfi gaba daya a yi maganin wannan fitina, su kansu hukumomi na kawo agaji kamar su NEMA. Su ma an ba su umurnin su hada kansu su bada gudunmawa mussaman ga wasu al’ummar Najeriya da suka ketara jamhuriyar Nijar don samun mafaka daga fiitina.

A halin yanzu ana kokarin daukar tsauraran matakan tsaro da za su ba wa jama’a damar dawo wa garuruwansu domin su ci gaba da rayuwa kamar kowa.

Malam Garba Shehu ya ce an yi nasara wajen dakile da’addanci a Najeriya idan aka yi dubi da yadda abun yake ada, ya kuma ce gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata domin ta dakile hare-haren yan bindiga.

Ga cikkaken Tattaunawar:

Your browser doesn’t support HTML5

GARBA SHEHU: Gwamnati Na Iya Bakin Kokarinta Wajen Dakile Yan-Bindiga