Gwamnatin Najeriya Ta Bude Makarantu

Shugaba Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba da umarnin bude makarantu da dage dokar takaita zirga-zirga tsakanin jihohi a duk fadin kasar, a wani mataki na fara sassauta dokar takaita zirga-zirga wacce aka saka domin yaki da annobar Coronavirus.

To sai dai wadanda suke kokarin kammala makaranta ne kawai za su iya komawa, wato yaran da ke ajin karshe a kowane mataki na makarantu wadanda masu yi jarabawa.

An kuma bayyana cewa jiragen sama zasu fara tashi a tsakanin jihohi a kasar, sai dai ba a bayyana lokacin hakan ba.

Shugaban kwamitin babban kwamitin yaki da cutar COVID-19 na kasar, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a taron da aka yi a Abuja yau Litinin.

Ya bayyana cewa an cimma hakan ne a yayin kashi na 5 na rahoton farko na kwamitin da aka gabatarwa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.

Sai dai gwamnati za ta tsawaita kashi na 2 na sassauta dokar zama a gida na makonni hudu, daga gobe Talata 30 ga watan Yuni har zuwa Litinin, 27 ga watan Yuli.