Gwamnatin Najeriya Ta Amince Da Matakin Korar Walter Onnoghen

Lauyoyin dake kare Walter Onnoghen a kotu.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi na’am da hukuncin da kotun da’ar ma’aikata ta yankewa tsohon Alkalin Alkalai Walter Onnoghen.

Kotun da’ar ma’aikata ta kama Walter Onnoghen da laifin mallakar dukiyar da ta zarce hankali, kuma aka kwace ta aka mayar ga gwamnatin tarayyar Najeriya. Haka kuma an sauke shi daga mukaminsa tare da hana shi rike kowanne irin mukami har sai bayan shekaru 10.

Gwamnatin tarayya ta fito fili ta goyi bayan hukuncin da aka dauka akan Alkalin Alkalai, tana mai cewa wannan babban darasi ne ga sauran Alkalai da lauyoyi da sauran ‘yan kasa wadanda za a iya kamawa da laifukan cin hanci da rashawa.

Tun farko dai Majalisar masu shari’a ce ta baiwa shugaba Buhari shawara kan ya sauke Alkalin Alkalai daga kan aiki, domin a kare mutuncin shari’a da mutuncin ‘kasa.

Domin jin cikakken rahotan saurari rahotan Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya Ta Amince Da Matakin Korar Walter Onnonge - 4'00"