Gwamnatin Najeriya Na Zargin ‘Yan adawa Da Kokarin Ta Da Husuma

Ministan yada labarai na Najeriya, Lai Mohammed a lokacin da ya kai ziyara makarantar Dapchi

Gwamnatin Najeriya ta yi zargin cewa ‘yan adawa na kulle-kullen ta da fitina a lokacin babban zaben watan gobe a wasu jihohin kasar.

Hukumomin na zargin cewa a wasu jihohin arewacin kasar 10 ake kokarin ta da husuma da hakan ya hada da shigo da tsageru daga Jamhuriyar Nijar.

Ministan labarun Najeriya Lai Muhammed, ya ce ‘yan adawa sun hada kai har da ‘yan Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda inda za su kai hari kan wasu gwamnoni baya ga shigo da makamai daga ketare.

Jam’iyyar APC a na ta bangaren ba ta musanta wannan matsayi na sashenta na zartarwa ba, inda ta ce aikin jami’an tsaro ne su bankado masu son ta da zaune tsaye.

Mataimakin shugaban jam’iyyar, Sanata Lauwali Shu’aibu, ya bayyana matsayin jam’iyyar da hakan ke nuna mara baya ga matsayar gwamnatin.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da zargin inda ta nuna gwamnatin ta gaza cika alkawarin murkushe Boko Haram don haka ta ke kawo irin wannan zargi.

Sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Umar Tsauri, ya maida martanin ya na mai cewa duk ragamar tsaro ta na hannun masu mulki ne.

In za a tuna tsohon shugaba Jonathan a littafin tarihin jagorancinsa, ya ce cikin zargin da aka yi ma sa, akwai kirkiro Boko Haram don rage yawan jama’ar arewa da ya nuna cewa, ya kamata a ga bayan ‘yan ta’addan tun da yanzu ba shi ne a karagar mulki ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya Na Zargin ‘Yan adawa Da Kokarin Ta Da Husuma -2'48"