A jiya ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da wani shiri da zai kawo karshen kowanne irin nau’in bauta da fataucin mutane dake faruwa a Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce rahotanni na nuni da cewa kashi ashirin da biyar cikin yara miliyan tamanin, ‘yan kasa da shekaru goma sha hudu dake Najeriya, wato yara miliyan ashirin, na fuskantar barazanar fadawa ayyukan karfi don biyan bukatun su.
Akan haka ya sa gwamnatin tarayyar Najeriya ta tsara wasu shirye-shirye da zasu taimaka wajen kawo karshen ayyukan tilas, bauta, da haramta fataucin yara da hana tilasta musu shiga aikin sojin sa-kai nan da shekara ta dubu biyu da ashirin da biyar.
Madam Hannatu Shehu, ta ce sau da dama talauci da rashin tawakali ke sa iyaye sanya ‘yayansu bauta.
Ita kuma Hajiya Maimuna Sa’id, ta ja hankalin iyaye akan su nemi sana’o’in da zasu iya tallafa wa iyalansu.
Darakta a ma’aikatar mata da walwalar jama’a a jihar Filato, Mr. Joseph Gwesam yace wayar da kan iyaye kan illar mika yaransu bauta da samar da makarantu kyauta zasu taimaka wajen kawo karshen matsalolin a cikin al'umma.
Ga karin bayani cikin sauti daga Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5