Gwamnatin Najeriya Na Kashe Naira Biliyan Shida Akan Matasa Duk Wata

Shirin N-Power

Yayin da wasu jihohin Najeriya ke korafi kan shirin samar da aikin wucin gadi da gwamnatin kasar ta kirkiro dashi watau N-Power ke tafiyar hawainiya, yanzu haka jami’an kula da shirin na gudanar da wani ziyarar gani da ido, inda suka isa jihar Taraba inda anan ma ake kokawa.

Gwamnatin kasar dai tace ta na kashe zunzurutun kudin daya kai Naira biliyan shida a kowani wata kan shirin aikin wucin gadin da take yi na N-Power, da zammar magance rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Yayin ziyarar gani da ido na yadda shirin ke gudana a jihar Taraban, hadimin shugaban kasa kan harkokin samar da ayyukan yi, Mr Afolabi Inmokhide ya yaba da yadda matasa ke son runguman shirin na N-Power wanda yace an kirkiro da shirin ne da zammar magance zaman kasha wando .

Hadimin ya shawarci matasan dake cin gajiyar shirin da su tabbatar sun yi adashen gata da wani abu daga cikin Naira dubu talatin (N30,000), din da ake basu na alawus din wata-wata.

Yace ,’’ munzo ne muga yadda shirin ke tafiya kamar sauran jihohi, kuma manufar wannan shiri shine na samar da ayyukan yi inda wasu za’a tura su makarantu ,da wasu wurare da kuma harkar noma kamar yadda muka tarar, don haka ya kamata a maida hankali domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

A jihar Taraba dai fiye da mutum dubu uku ne aka dauka a wannan shiri inda tuni har wasu sun soma karbar alawus, yayin da wasu fiye da dubu daya kawo yanzu ko da kwandala basu samu ba batun da ya kai wasunsu yin zanga-zangar lumana.

To sai dai da take Karin haske mai kula da shirin a Taraba wato Mrs Beatrice Kitchina ta nuna farin cikinta da ziyarar tawagar daga Abuja da tace zai kawar da zargin da tun farko ake yi musu na cewa an yi wakaci-ka-tashi ne da kudaden.

Samar da aikin yi dai na cikin burorin gwamnatin Buhari, data ce zata cimmawa kafin karshen wa’adin shekaru hudu,wanda kuma lokaci ne kawai ke tabbatar da hakan.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya Na Kashe Naira Biliyan Shida Akan Matasa Duk Wata - 3'00"