Gwamnatin Legas Ta Rufe Makarantun Chrisland Don Gudanar Da Binciken Zargin Lalata

Makarantar Chrisland a Legas

Gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Chrisland da ke jihar nan take, har sai an kammala gudanar da bincike kan zirgin cin zarafin wata dalibar makarantar a badalance, yayin wata tafiya da suka yi zuwa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

A cewar rahotani, rufe makarantun na Chrisland da aka yi a fadin Legas, an yi ne domin a ba da damar gudanar da bincike mai inganci kan zarge-zargen da ake yi na cin zarafin dalibar da abokanenta da kuma sauran abubuwan da suka shafi lalata da aka yi a lokacin balaguron.

Kwamishiniyar Ilimi, Folashade Adefisayo, ita ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, yayin da ta ke mayar da martani kan zargin.

A cewar sanarwar, an yi hakan ne domin tabbatar wa al’umma kudurin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaro da kare yara, musamman wajen tabbatar da cewa dukkanin cibiyoyin da suka shafi yara a jihar, su na aiwatar da tsare-tsare da suka dace da Dokar Zartaswa na(NO.EO/AA08 na 2016) wato Shirin Kare Yara na Jihar Legas.

Ku Duba Wannan Ma Hukumomin Nijer Sun Kadamar Da Shirin Bude Cibiyoyin Karatun Yaran Da Matsalar Tsaro Ta Janyo Rufe Makarantu

“Muna amfani da wannan kafar don tunatar da jama’a cewa duk mutumin da ya aikata duk wani abu na batsa da ya shafi yaro, ko ya aikata laifi, zai fuskanci hukuncin daurin shekaru goma sha hudu (14). Wannan ya haɗa da "samar da, rarrabawa, karɓa, ko mallakar hoton batsa na yara".

Gwamnati ta bayyana cewa ta tura hukumomi daban-daban domin gudanar da bincike kan wannan zargi, kuma an sanar da hukumar ‘yan sandan Legas game da lamarin

“Yana da kyau a lura cewa ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa suna binciken dukkan zarge-zargen da suka hada da ma’aikatar ilimi, ofishin tabbatar da ingancin ilimi, ma’aikatar matasa da ci gaban jama’a, ma’aikatar shari’a da kuma harkokin cikin gida ta jihar Legas.

Ta kuma kara tabbatar wa ‘yan Legas yunkurin da suke yi wajen kare ‘yancin yara da kare lafiyarsu, kuma duk wanda aka samu da laifin keta su zai fuskanci shari’a yadda ya kamata.

-Channels Television