Kafin su fara gamganmin ne ministan tsaro na kasar jamhuriyar Kamaru, ya umarci jami’an tsaro da su tarwatsa al’ummar dake shirin wannan taro. Wakilin Muryar Amurka, Garba Awal ya nemi jin ta bakin wani dan wata kungiya mai sanya ido kan harkokin gwamnatin Kamaru.
Wanda ya bayyana cewa kungiyar dai sun dauki aniyar rubuta sunayen mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon Boko Haram kan wani babban allo, yace an hada sunaye 1262 wanda suka hada da sunayen fararen hula da dakarun soja domin a nunawa jama’a.
Sai dai Alhaji Mijin Yawa, sakataren hukumar kula da yin gangami a jihar Yaounde, yace “maganar ayi taro bashi bane matsalar ba, to mai zai biyo baya a taron? Muna kan bincike muga idan gaskiya ne abin da suka ce don su yabawa sojoji ne yasa zasuyi.
Your browser doesn’t support HTML5