YAOUNDE, KAMARU: Ministan lafiya na kasar Kamaru Malachie Manaouda ya yi Allah wadai da wasu ‘yan Kamaru da yawa da sa son amfani da gidan sauro wanda ƙasar ke bayarwa kyauta, a kokarin yaki da cutar zazzabin cizon sauro.
Yayin da Kamaru ke cikin ƙasashe 11 da suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauro a duniya, gwamnatin ƙasar ta ƙaddamar da wani gagarumin aikin raba gidan sauro mai suna Milda.
Wasu sun ce ba su damu da gidan sauron ba saboda yana takura su. Suna cewa kamata yayi gwamnati ta nemi hanyoyin magance talauci don jama'a su samu sauki.
Ƙasar ta kaddamar da shiri ne don raba gidan sauro sama da miliyan 16 da dubu dari 5 domin kare ɗaukacin al'ummarta. A ranar 7 ga watan Yuni aka fara aikin a Pitoa da ke yankin arewacin ƙasar, wanda ke ɗaya daga cikin yankunan da cutar zazzabin cizon sauro ta fi shafa.
Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa sauro nau'in Anopheles da ke yaɗa cutar zazzabin cizon sauro, a shekaru baya ya iya jure wa sinadiran da ke cikin gidan sauron amma na yanzu suna dauke da pyrethroid da chlorfenapyr, wato sinadiran da ba a taba amfani da su ba. An riga an tabbatar da waɗannan gidajen sauron a kasar Tanzaniya, a cewar hukumar WHO.
Da wannan sabon aikin na raba gidajen sauro, gwamnatin na fatan rage yawan mace-macen da ake samu sakamakon zazzabin cizon sauro wanda a bara ya lakume rayukan 'yan Kamaru fiye da 3,800.
Saurari rahoton Muhammad Bachir Ladan cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5