Jami’ai a Kafar yada labarai ta Petra sunce goma daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin, yan ta’adda ne wadanda laifuffukansu suka hada da Kisan gillar wani marubuci, da kuma harin Bam a ofishin jakadancin Jordan dake Baghdad da kuma harin ta’addanci kan Masu yawon bude ido na kasashen waje a wurin da ake kira Roman Amphitheater a babban birnin Jordan wato Amman.
Saura biyar kuwa an yanke musu hukuncin ne sakamakon munanan laifuffukan da suka hada da Fyade.
Gaba dayan masu laifin an rataye su a faduwar rana a gidan yari mai suna Swaqa, wanda yake kilomita 70 Kudu da Amman.
Kasar Jordan dai ta dakatar da hukuncin Rataya tsakanin shekarar 2006 zuwa 2014 amma ta dawo da gudanar da hukuncin kisa sakamakon karuwa munanan laifuka da alumma suka zargi faruwar hakan sakamon dage dokar.