Gwamnatin Jamhuriyar Kamaru ta sake karfafa matakan tsaro a jihohin yankin Ingilishin kasar guda biyu, wato jihohin Baminda da Boya.
Gwamnatin za ta dauki matakin ne saboda yadda ake kashe tare da sace 'yan sandan kasar a jihohin biyu.
Haka kuma ana yin garkuwa da manyan jami'an gwamnati a yankunan.
Mr. Rawul wanda ya kasance shi ne mai bai wa ministan tsaro shawara akan rikicin bangaren 'yan awaren, ya bayyana irin matakan tsaron da suka dauka ko kuma za su dauka.
Ya ce gwamnatin Kamaru da ministan tsaro da su kansu suna ganin dole ne su inganta matakan tsaro su kuma kwato wani karamin magajin garin da aka yi garkuwa da shi.
Domin a cewarsa, hakki ne da ya rataya a wuyansu yana mai cewa, wajibi ne su kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu.
Saurari rahoton Muhammad Awal Garba domin jin karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5