Gwamnatin kasar Jamhuriyar Kamaru ta karfafa matakan tsaro a jihohin Ingilishin kasar guda biyu inda ta ce masu tada kayar baya na neman dara kasar gida biyu.
Cikin 'yan kwanakin nan an samu wasu matasa suna yiwa dakarun kasar kisan dauki dai dai.
Alhaji Ibrahim Maiyaki wani dan siyasa wanda yake zaune a garin Mafe a yankin Ingilishin kasar ya zanta da Muryar Amurka akan abun dake faruwa. Ya ce inda aka kashe sojoji hudu sai gwamnatin kasar ta tura dakaru da dama lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. Cikin kwanaki biyun da suka gabata an kone kasuwar Mafen. Baicin hakan an mamaye sararin samaniyarsu da jirage masu saukan angulu kana wata hanya da ta baci tun da dadewa sojoji sun gyara domin su samu wucewa suna kaiwa jama'ar Ingilishi hari.
A cewar Alhaji Ibrahim Maiyaki babu wani batun 'yan ta'adda. Wadanda aka ki a zauna a tattauna dasu ne ake kira 'yan ta'adda. Ya ce su basu da wata matsala. Gwamnati ce ta ki sauraronsu. Ta yi banza da maganarsu. Ba ta son ta yi magana dasu duk da cewa duniya gaba daya ta ce a zauna a tattauna da yankin Injishi. Sai dai gwamnatin Kamaru ta yi kememe, ba zata zauna a teburin shawara ba. A bangaren Ingilishi idan ba 'a zauna a tattauna ba ba za'a samu zaman lafiya ba, inji Maiyaki.
A bangaren Ingilishin, harkokin karatu da kasuwanci da samun walwalar rayuwa duk sun tsaya cik sai dai wasu matasa da suke aiwatar da aikin tsaro.
Ga Muhammad Awal Garba da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5