Wannan shi ne karo na farko da gwamnatin jihar zata dauki irin wannan matakin.
Gwamnatin zata dinga raba kayan abinci ga masu kananan karfi. Gwamnan jihar Kashim Shettima ya kaddamar da shirin a unuguwar Gumari cikin birnin Maiduguri.
Gwamnan ya bukaci jama'a da su cigaba da addu'o'i domin Ubangiji ya kawo karshen rigingimun da jihar ta tsinci kanta a ciki wadanda suke son su gagari jihar.
Za'a ba mutane dubu hamsin kayan abincin da suka hada da shinkafa da mai da burabisko. Gwamnan yace mutanen da suka cancanta su samu abinci ya kamata a basu. Ya roki jama'a su raba abincin ba tare da hayaniya ba ko hargitsi. Yace daga yanzu zasu cigaba da tallafawa mutane iyakar kokarinsu.
Alhaji Girema shugaban hukumar dake samarda agajin gaggawa ta jihar Borno yace gwamnan ya shirya tallafin ne sabili da irin wahalar da jama'arsu suke ciki. Yace zasu yi anfani da shugabannin unguwani inda kowace unguwa zata zabi mutane hamsin wadanda zasu raba kayan.
A karon farko kowace unguwa zata samu kayan abinci na mutane dari shida.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5